Shugabancin Harkokin Addini na Turkiyya ya tura wata babbar tawaga don samar da cikakkun tsare-tsaren udanar da ayyuka ga mahajjatan Turkiyya yayin Aikin Hajjin bana.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Makka ranar Laraba, shugaban hukumar, Ali Erbas, ya sanar da cewa Turkiyya ta tura mahajjata 84,942 zuwa Saudiyya don Aikin Hajji a wannan shekarar.
Yawancin mahajjatan Turkiyya sun riga sun isa biranen Makka da Madina, yayin da sauran suke kan hanyar zuwa biranen masu tsarki a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Matsakaicin shekarun mahajjatan Turkiyya shi ne 60, wanda ke nuna cewa mafi yawansu tsofaffi ne masu ƙwarewa a wannan tafiya ta ibada.
Erbas ya bayyana Aikin Hajji a matsayin “wani lamari mai cike da ƙalubale amma kuma ita ce ibada mai matukar ma’ana,” tare da jaddada shirin da Shugabancin ya yi a fannoni daban-daban kamar jagoranci, lafiya, da tallafin kayan aiki.
“Muna gudanar da babbar kungiya don tabbatar da cewa ‘yan ƙasarmu za su iya cika ayyukan Hajjinsu cikin mafi kyawun yanayi,” in ji Erbas.
Ya bayyana cikakken tsarin tallafi wanda ya haɗa da jagorancin addini, ayyukan lafiya, masauki, sufuri, da sadarwa.
An tura malamai kwararru 71 da jagororin addini mata 418 don gudanar da ayyukan irshad (jagorancin ibada), tare da shugabannin rukuni 392 da mambobi 1,840 don hidimta wa mahajjatan.
“Muna kallon Aikin Hajji ba kawai a matsayin ibada ba, amma a matsayin tafiya mai zurfi ta ilimi da ruhaniya,” in ji shi. “Muna son kowane mahajjaci ya dawo gida tare da ci gaban ƙashin kansa da na al’umma.”
An kammala shirye-shiryen Hawan Arfa, daya daga cikin muhimman sassan aikin Hajji. Erbas ya ce an girka tantuna masu sanyaya yanayi kuma ana kafa wani asibiti na wucin gadi don kula da mahajjatan da suka kamu da rashin lafiya ko tsofaffi.
“Ko da yake ba daɗewa za mu yi a can ba, mun kuma kafa wani asibiti na wucin gadi don amsa duk wata bukatar lafiya, musamman ga tsofaffi da masu nakasa, wadanda za a kula da su ta hanyar sufuri ta mota kawai,” ya kara da cewa.
Bugu da ƙari, tawagar Diyanet Digital, ofishin watsa labarai na Shugabancin, da tashar talabijin suna nan a ƙasa mai tsarki don taimakawa wajen watsa labarai da sadarwa.
Ƙarfin hadin gwiwa da Saudiyya
Erbas ya kuma bayyana godiyarsa ga Saudiyya saboda ƙarfin haɗin-gwiwa da goyon baya. “Muna da kyakkyawar dangantaka ta aiki da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya.
Sadaukarwarsu wajen hidimta wa mahajjata abin yabo ne, kuma ina so in miƙa godiyata zuwa ga ‘yan’uwanmu a wannan ƙasa mai abokantaka da zumunci,” in ji shi.