Duniya

Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga Pakistan kan mutuwar ɗaruruwan ‘yan ƙasar a ambaliyar ruwa

Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga ƙasar Pakistan kan mutuwar ‘yan ƙasar sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a yankuna daban-daban na ƙasar.

Newstimehub

Newstimehub

16 Aug, 2025

9a41b4ca16b05237c7a24f4fc53178bf143641e3c8ff0e94935efa341c6ad1bd

Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga ƙasar Pakistan ranar Asabar sakamakon mutuwar ɗaruruwan ‘yan ƙasar a ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar.

“Muna matuƙar baƙin ciki game da rasa rayukan da aka yi sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan,” a cewar wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

Ta ƙara da cewa: “Muna addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma muna miƙa ta’aziyyarmu ga Pakistan.”

Hukumomi a Pakistan ranar Asabar sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya zarta 321.