Wani jirgin Amurka samfurin KC-135 ya faɗi a yammacin Iraƙi yayin da wani ya sauƙa lafiya, in ji rundunar sojin Amurka.
“Ɗaya daga cikin jiragen ya faɗi a yammacin Iraƙi, kuma ɗayan ya sauƙa lafiya. Ba abokan gaba ne suka harbo jirgin ba,” in ji cibiyar tsaron ta Amurka (CENTCOM), wadda ke da alhakin kula da dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya, in ji sanarwar.
Jirgin samfurin KC-135 shi ne aƙalla jirgin Amurka na huɗu da aka rasa yaƙin Iran, bayan an harbo jirage samfurin F-15 uku da a sararin samaniyar Kuwait.
Jiragen KC-135s, waɗanda suka shafe fiye da shekaru 60 suna aiki, sukan ɗauki ma’aikata uku ne: matuƙan jirgi biyu da kuma wanda yake sarrafa bututun da ake amfani da shi wajen bai wa sauran jirage mai, in ji rundunar sojin saman Amurka.
Amma wasu ayyukan KC-135 na buƙatar na’urar gane-mini-hanya, kuma jirgin zai iya ɗaukar fasinjoji 37, kamar yadda wata takardar bayanai ta rundunar sojin sama ta bayyana.
Da farkon yaƙin, wanda aka fara ranar 28 ga watan Fabrairu, dakarun Kuwait sun kakkaɓo jirgagen yaƙin Amurka samfurin F-15E, amma dukkan jami’an cikin jiragen shida sun iya fitar da kawunansu, in ji CENTCOM.
Wancan lamarin ya auku ne a lokacin yaƙi, ciki har da “hare-hare daga jirgin saman Iran da makamai masu linzami da jirage mara matuƙa,” in ji rundunar ta soji a wancan lokacin.














