Alonso ya yi shelar ‘sabon zamani a Real Madrid’

An naɗa Alonso, mai shekara 43, a matsayin kocin kulob ɗinsa na da a kan yarjejeniyar shekara uku ranar Lahadi inda ya maye Carlo Ancelotti – wanda zai ja ragamar tawagar ƙwallon ƙafa ta Brazil.
26 May, 2025
Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya a kakar bana

Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni huɗu a kammala gasar.
24 May, 2025
Luka Modric ya aike da sakon bankwana ga masoya Real Marid

Dattijon ɗan wasan tsakiya na Real Madrid zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana, bayan shafe shekaru 13 yana taka mata leda.
22 May, 2025
Kocin Man United ya ce a shirye yake ya ajiye aiki bayan shan kaye a Gasar Europa

Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya ce yana da imanin kan ƙarfinsa na kawo gyara a ƙungiyar, duk da cewa a shirye yake ya ajiye aiki bayan da suka gaza ɗaukar kofin Europa League.
22 May, 2025

Guardiola ya ba da sharaɗin ci gaba da zama Kocin Man City

Ana sa ran samu ƙarin mata a kyautar Ballon d’Or ta 2025

Ana sukar Messi saboda ya ce alkalan wasa a Amurka ‘ba su iya alkalanci ba’

Shugaban Barcelona ya ce bai hakura da neman ɗauko Haaland ba

Messi ya taya Barcelona murnar lashe kofin La Liga na bana
15 May, 2025
Jamie Vardy zai bar Leicester City bayan ya buga wasansa na 500 a kungiyar
Tauraron ƙungiyar Leicester City ta Ingila, Jamie Vardy zai buga wasansa na ƙarshe a ƙungiyar ranar 18 ga Mayu, maimakon ranar da Leicester za ta buga wasan ƙarshe a gasar Firimiya ta bana.

14 May, 2025
Djokovic ya sallami kocinsa Andy Murray gabanin gasar tenis ta French Open
Andy Murray ya daina aiki da Novak Djokovic a matsayin mai horar da shi, bayan kwashe watanni shida ba tare da Djokovic ya yi nasarar cin kofi ba.

13 May, 2025
Ousmane Dembele ne gwarzon shekara na gasar Ligue 1 ta Faransa
Bayan nuna bajintar cin ƙwallaye a gasar gida ta Faransa da gasar Zakarun Turai, Ousmane Dembele ya jagoranci PSG wajen lashe kofin Ligue 1 da na French Super Cup.

13 May, 2025
Taiwo Awoniyi: An yi wa dan wasan Nottingham Forest dan asalin Nijeriya tiyata
Ɗan wasan Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi ya samu rauni lokacin da ya yi taho-mu-gama da turken raga a wasan da Nottingham Forest ta buga da Leicester ranar Lahadi.

12 May, 2025
Nijeriya ta kai wasan dab da na karshe a gasar U20 ta Afirka, za ta je gasar FIFA U20 ta duniya
Tawagar ƙwallon Nijeriya ta ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta doke ta Senegal a wasan kwata-fainal na kofin Afrika na CAF U20 da ke gudana a Masar, inda kuma ta cancanci zuwa gasar duniya ta FIFA U20.

9 May, 2025
Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon shekara a Ingila karo na 3
Tauraron ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan shekara a Ingila, wanda Ƙungiyar Marubuta Wasanni ta Ingila ta zaɓa a bana.

9 May, 2025
Lamine Yamal na kaunar buga kwallo a Man U da Liverpool
Haziƙin ɗan ƙwallon ƙafar Sifaniya, Lamine Yamal, wanda tauraruwarsa ke haskawa a ƙungiyarsa ta Barcelona da tawagar Sifaniya, ya bayyana sha’awarsa ta buga wasa a Ingila.

6 May, 2025
Arsene Wenger na son a hana Man U ko Tottenham buga Gasar Zakarun Turai
Tsohon kocin Arsenal kuma mai ba wa hukumar ƙwallo ta duniya FIFA shawara, Arsene Wenger yana so a duba yiwuwar daina bai wa ƙungiyar da ta ci kofin Europa damar buga Gasar Zakarun Turai.

2 May, 2025
Kofin Afirka na U20: Auwal Ibrahim ya samar wa Nijeriya nasara kan Tunisia a wasan farko
Sakamakon ya bai wa Nijeriya maki uku muhimmai a rukunin da ke da ƙasashen Morocco da Kenya.

30 Apr, 2025
Al-Hilal na neman Ancelotti domin janyo hankalin Vinicius daga Real Madrid
Al-Hilal ta Saudiyya ta fara ƙoƙarin ɗaukar kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti don kyautata damarsu ta jan hankalin Vinicius Junior ya baro Real Madrid.



