Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) za ta bai wa ’yan fitar da kaya na Najeriya wata muhimmiyar kafa ta shiga kasuwannin duniya, musamman yankin Gulf da sauran ƙasashe.
Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata hira a shirin Politics Today na Channels Television, bayan rattaba hannu kan Comprehensive Economic Partnership Agreement (CEPA) tsakanin Najeriya da UAE.
A cewar ministar, yarjejeniyar ta bai wa kayayyaki sama da 7,000 daga Najeriya damar shiga kasuwar UAE ba tare da biyan harajin shigo da kaya ba, ciki har da magunguna, sinadarai da kayayyakin noma.
“Mun so ’yan kasuwar Najeriya su yi anfani da wannan dama. Kayayyaki sama da 7,000 za su shiga UAE ba tare da haraji ba,” in ji ta.
Oduwole ta ce an zaɓi UAE ne da gangan saboda muhimmancinta a harkar kasuwancin duniya. Ta bayyana ƙasar a matsayin cibiya da ke haɗa Gabas da Yamma, tare da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ƙasashen kasuwanci a duniya.
A cewarta, yarjejeniyar za ta ba ’yan kasuwar Najeriya damar buɗe ofisoshi da rassa a UAE, yayin da ’yan kasuwa za su iya zama a ƙasar har kwanaki 90 cikin shekara guda.
Ministar ta ƙara da cewa Najeriya za ta ƙarfafa fitar da kayayyakin da take da ƙwarewa a kansu, inda za a yi amfani da UAE a matsayin kasuwa da kuma matattarar fitar da kaya zuwa sauran ƙasashen duniya.
Ta kuma bayyana cewa yarjejeniyar za ta jawo zuba jari daga UAE zuwa Najeriya, musamman a bangaren ginshikin rayuwa, masana’antu da makamashi, inda Najeriya za ta zama cibiyar da za a rika kai kayayyaki zuwa sauran Afirka.
Oduwole ta ce ’yan kasuwar Najeriya za su iya fara fitar da kaya nan take, yayin da sauran tanade-tanaden yarjejeniyar za su fara aiki a hankali cikin shekaru uku zuwa biyar.
A wani bangare, ministar ta ce Afirka na matuƙar buƙatar kayayyakin Najeriya, inda ta ambaci buɗe hanyar jigilar kaya ta sama tare da Uganda Airlines, wadda ta haɗa ƙasashe 13 na Gabas da Kudancin Afirka.
Ta ce kayayyakin da ake buƙata sun haɗa da abinci da aka sarrafa, kayan sha, kayan ado da tufafi, tana mai cewa kasuwar Afirka “na jin yunwa da ƙishirwa” ga kayayyakin Najeriya.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar Najeriya da UAE ne a ranar Talata a yayin Abu Dhabi Sustainability Week 2026, inda Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yarjejeniyar na goyon bayan zuba jari mai tsafta, haɓaka fitar da kaya marasa man fetur da bunƙasar tattalin arziki na dogon lokaci.














