Gabas Ta Tsakiya

Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu ta buƙaci Iran ta guji kai hari kan ƙasashe maƙwabta

A cikin wata buƙata wadda ba a saba gani ba daga ƙungiyar ta Hamas a ranar Asabar, ta jaddada haƙƙin Iran na kare kanta daga Isra’ila da Amurka amma ta buƙaci ta guji kai hari ƙasashe maƙwabta.

Newstimehub

Newstimehub

14 Mar, 2026

emirates iran us israel 17766

Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa ta Hamas, ta yi kira ga Iran da ta guji kai hari ƙasashe maƙwabta, yayin da take jaddada haƙƙin Tehran na kare kanta daga Isra’ila da Amurka.

A cikin wata buƙata wadda ba a saba gani ba daga ƙungiyar a ranar Asabar, Hamas ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya su ɗauki matakai don kawo ƙarshen yakin da ya mamaye Gabas ta Tsakiya wanda aka fara tun a ranar 28 ga Fabrairu.

“Yayin da muke jaddada haƙƙin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da martani ga wannan farmaki ta duk hanyoyin da ake da su bisa ga ƙa’idoji da dokokin ƙasa da ƙasa, ƙungiyar na kira ga ‘yan uwanta a Iran da su guji kai hari kan ƙasashe makwabta,” in ji Hamas a cikin wata sanarwa, wanda wannan shi ne kira irinsa na farko ga Tehran a bainar jama’a.

Hamas, wadda ta shafe fiye da shekara biyu tana yaƙi da Isra’ila a Gaza, ta kuma yi kira ga al’ummar duniya da “su yi aiki don dakatar da” yakin da ke ci gaba nan take.

Kungiyar a baya ta yi tir da kisan Jagoran Addini na Iran, Ali Khamenei, a ranar farko ta fara yakin inda ta bayyana kisan a matsayin “babban laifi”, tare da bayyana cewa ya jima yana goyon bayan gwagwarmayar neman ‘yancin Falasɗinawa.

“Ya samar da dukkan nau’ukan tallafin siyasa, diflomasiyya da na soja ga mutanenmu da gwagwarmayarmu,” kamar yadda ƙungiyar ta bayyana jim kaɗan bayan kisan Khamenei.

Wani jami’in Hamas ya shaida wa AFP cewa ƙungiyar ta kasance tana tuntuɓar jami’an Iran game da wannan batu.

“Mamayar Isra’ila na neman jefa ƙiyayya tsakanin Iran da makwabtanta Larabawa da Musulmi,” in ji majiyar, wanda ya yi magana a sharaɗin rashin bayyana sunansa saboda ba shi da izinin ba da bayani ga kafafen watsa labarai.

Duk da dai munanan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai mata, Iran ta rinƙa mayar da martani ta hanyar amfani da makamai masu linzami a kan ƙasashe aƙalla goma.