An katse ayyukan intanet da wayoyin hannu a faɗin Iran, kamar yadda ƙungiyar sa ido kan intanet ta NetBlocks ta tabbatar.
Rahotanni sun nuna cewa katsewar ta fara ne jim kaɗan bayan tsanantar zanga-zangar da ta barke tun daga ƙarshen Disamba, wadda ta samo asali daga matsalolin tattalin arziki da faɗuwar darajar kuɗin Iran.
Zanga-zangar ta bazu daga Tehran zuwa wasu manyan birane, inda wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 38, kodayake hukumomin Iran ba su tabbatar da hakan ba. A gefe guda, Tehran ta zargi Amurka da tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar.














