Nijeriya

‘Yanbindiga sun kashe Kanar na sojin Nijeriya bayan ya ƙi amincewa su yi garkuwa da shi

Abdussalam Ude, wanda Kanar ne a rundunar sojin Nijeriya, ya yi turjiya ga maharan duk da cewa suna da yawa, lamarin da ya jawo maharan suka harbe shi har lahira.

Newstimehub

Newstimehub

29 Jul, 2026

9999cd7b 093d 4a81 9302 026c2bdd50c6 1785319253690

Sashen Tattara Bayanan Sirri na Rundunar Tsaron Nijeriya ya tabbatar da kashe ɗaya daga cikin manyan sojojinsa wato Kanar Abdussalam Ude wanda ya rasu bayan wasu ‘yanbindiga sun harbe shi yayin da ya yi ƙoƙarin hana su sace shi a gidansa da ke unguwar Kurudu a Abuja. a gidansa da ke unguwar Kurudu a Abuja.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin jim kaɗan bayan babban jami’in ya isa gidansa. Rahoton ya ce maharan sun buɗe masa wuta yayin da yake fitowa daga motarsa kafin su yi ƙoƙarin yin garkuwa da shi.

Ude, wanda ke riƙe da muƙamin Kanar a rundunar sojin Nijeriya, ya yi turjiya ga maharan duk da cewa suna da yawa, lamarin da ya hana su yin garkuwa da shi.

Sai daga bisani maharan suka harbe shi sau da dama daga kusa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Harin ya kuma jikkata matar jami’in da direbansa da wani mai gadi, inda suka samu raunukan harbin bindiga. An garzaya da su asibiti kuma suna karɓar magani.

A sanarwar da Sashen Tattara Bayanan Sirri na Rundunar Tsaron Nijeriya ya fitar, ya ce tuni aka fara gudanar da bincike domin ganowa da kuma kama waɗanda ke da hannu a kisan.

Kurudu, inda lamarin ya faru, na wajen birnin Abuja kuma dubban mutane ne ke zaune a yankin, ciki har da manyan jami’an sojoji da ƙananan sojoji.  

An sha samun hare-haren garkuwa da mutane a babban birnin Nijeriya, musamman a al’ummomin da ke bayan gari. Hukumomin tsaro sun kuma kama mutane da dama da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da mutane a birnin.

A cewar PRNigeria, Mista Ude ya taɓa aiki a muhimman sassan leƙen asiri da yaƙi da ta’addanci a rundunar sojin Nijeriya. An ce ya halarci ayyukan yaƙi da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabashin Nijeriya, sannan ya gudanar da wasu muhimman ayyuka na musamman a ƙasashen Chadi da Faransa.

Har yanzu ana ci gaba da bincike kan yadda harin ya faru, yayin da hukumomin tsaro suka fara ƙoƙarin ganowa tare da cafke waɗanda suka aikata laifin.

Marigayin, wanda ya fito daga Jihar Enugu, ana sa ran za a ɗaga shi zuwa muƙamin Birgediya Janar a shekara mai zuwa. An shirya yi masa jana’iza a ranar Talata a Masallacin Mambilla da ke Abuja bisa tsarin Addinin Musulunci.