Aƙalla mambobi 10 na rundunar Popular Mobilisation Units (PMU) ta Iraki sun mutu a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Saudiyya kan sansanoninsu a sassa daban-daban na ƙasar, kamar yadda jami’ai biyu na ƙungiyar suka bayyana.
Lamarin na nuni da ƙarin tsananta rikicin da ya shafi ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke samun goyon bayan Iran.
PMU a ranar Laraba ta ce hare-haren sun afka wa wurare da dama na jami’anta, inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkata wasu da lalata gine-gine da sauran kadarori.
“Waɗannan hare-hare sun yi sanadiyyar shahadar wasu daga cikin jami’anmu da jikkatar wasu, tare da lalata gine-gine da kadarori da dama,” in ji ƙungiyar, wadda aka fi sani da sunan Hashd al-Shaabi a Larabci.
Wani jami’in PMU ya shaida wa AFP cewa harin da ya fi muni ya faru ne a lardin Nineveh, inda aƙalla mayaƙa 10 suka mutu, yana mai gargadin cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa.
Wani jami’i ya kuma tabbatar da cewa an samu asarar rayuka a wasu larduna, tare da tabbatar da adadin farko na waɗanda suka mutu.
Amurka da Saudiyya sun ce sun kai hare-haren kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai masu samun goyon bayan Iran a matsayin martani ga hare-haren da aka kai wa sojojin Amurka da cibiyoyin mai na Saudiyya.
PMU ta yi Allah wadai da hare-haren
PMU ta bayyana harin a matsayin “mummunan matakin da ya ƙara rura wutar rikici, take haƙƙin mallakar ikon Iraki, da kuma hari kan hukumomin tsaron ƙasar.”
An kafa PMU ne a shekarar 2014 domin yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh, daga baya kuma aka haɗa ta cikin rundunar sojojin Iraki.
Duk da cewa akwai ƙungiyoyi masu samun goyon bayan Iran a cikinta, da dama daga cikinsu na cin gashin kansu, kuma ana danganta su da hare-hare kan muradun Amurka a Iraki da sauran yankin.
Saudiyya ta zargi ƙungiyoyin masu samun goyon bayan Iran a Iraki da ƙaddamar da hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙa kan cibiyoyin mai da ke gabashin ƙasar, tana mai cewa tsarin kariyarta ya dakile harin.
Sai dai ƙungiyoyin sun musanta hannu a harin, inda suka ce Riyadh “ƙage”, ta yi musu tare da gargadin kada a ɗauki matakin soja a cikin Iraki.
Iraki na tsaka-mai-wuya tsakanin Amurka da Iran
Sabbin hare-haren sun sake nuna ƙalubalen da Iraki ke fuskanta wajen daidaita alaƙarta da manyan ƙawayenta biyu, Amurka da Iran, waɗanda rikicinsu ya sha mayar da ƙasar filin fafatawar yaƙi tsakanin ɓangarori biyu da ke rikici a bayan fage.
Firaminista Ali al-Zaidi, wanda ya hau mulki a farkon wannan shekarar, ya yi alƙawarin ƙara tsaurara ikon gwamnati kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai masu goyon bayan Iran tare da tabbatar da sun miƙa makamansu ga gwamnati, sai dai ya fuskanci adawa daga wasu manyan ƙungiyoyi masu tasiri.
Zaidi ya kai ziyara zuwa Washington da Tehran a farkon wannan watan a wani yunƙuri na rage zaman ɗarɗar da kuma kare zaman lafiyar Iraki.

















