Mutum aƙalla 30 ne suka mutu, ciki har da mata da yara, bayan wasu da ake zargi ‘yanta’adda ne sun kai hari a ƙauyen Naridon da ke Ƙaramar Hukumar Kauru a jihar Kaduna ta Nijeriya a safiyar ranar Litinin, kamar yadda mazauna da shugabannin al’ummar yankin suka bayyana.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kaduna, Shugaban SOKAPU, Tabara Kato, ya ce al’ummomin ƙananan hukumomin Kauru da Kajuru da Chikun da kuma Zangon Kataf na ci gaba da fuskantar barazana mai yawa daga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Ya yi kira da a sauya daga yin ɗaukar mataki bayan afkuwar hare-hare zuwa tsarin tsaro mai inganci ta hanyar tattara bayanan sirri da kuma isar jami’an tsaro cikin sauri a wuraren da ake kai wa hari.
Kazalika mazauna garin sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa maharan sun kai hari a Kamaru da ƙauyen Naridon da ke kusa da shi a yammacin ranar Litinin, inda suka buɗe wuta kan fararen-hula tare da ƙona gidaje.
Wani jami’in yankin Kamaru mai suna Dogon Rana, ya bayyana cewa yara takwas na daga cikin waɗanda aka kashe yayin da wasu huɗu suka jikkata, in ji Reuters.
Haka kuma wani mazaunin garin, Ishaya Dawa, ya ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da mata, da yara da tsofaffi, inda ya ƙara da cewa an kai wasu gawawwakinsu zuwa mutuware.
“Maharan sun isa da tsakar dare kana suka fara harbin mazauna garin, suka ƙona gidaje sannan suka gudu,” in ji Dawa.
Mazauna garin sun kokan kan jinkirin isowar jami’an tsaro, inda suka ce sojoji sun isa ƙauyen awanni da dama bayan harin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar ta Kaduna Mansur Hassan ya ce rundunar za ta bayar da ƙarin bayani kan lamarin, a cewar rahoton Reuters.
Martanin Gwamnati
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi Allah wadai da harin, tana mai bayyana shi a matsayin mummunar asarar rayuka da dukiyoyi.
Gwamna Uba Sani ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen gano waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu, a cewar mai magana da yawun gwamnatin jihar Ahmed Maiyaki.
Kazalika gwamnan ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da umartar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) da ta samar da kayan agaji da kuma ayyukan jinƙai ga al’ummomin da abin ya shafa.
Sabon harin ya sake haifar da damuwa game da matsalar rashin tsaro a sassan Jihar Kaduna, inda al’ummomin ƙauyuka da dama ke fuskantar hare-haren da kashe-kashe, da sace-sacen jama’a waɗanda ake dangantawa da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da masu ɗauke da makamai.

















