Gwamnatin Rasha ta fito fili ta musanta zargin cewa dakarunta sun kai hari kan ofishin jakadancin Qatar da ke birnin Kyiv, tana mai cewa barnar da aka gani ta samo asali ne daga matsalar tsarin kariyar sama na Ukraine, ba daga harin Rasha kai tsaye ba.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta fitar, ta jaddada cewa dakarun Rasha ba sa kai hari kan ofisoshin jakadanci. Ta ce wuraren da aka nufa ba su kusa da ofishin jakadancin Qatar, kuma abin da ya faru sakamakon rashin aiki yadda ya kamata na kariyar sama ta Ukraine ne.
Rasha ta kuma bayyana Qatar a matsayin abokiyar hulɗa mai muhimmanci, tana jaddada cewa dangantakarta da Doha ta dogara ne kan mutunta juna da haɗin kai.
Wannan bayani na zuwa ne bayan shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce wani jirgin yaki mara matuki (drone) ya lalata ofishin jakadancin Qatar yayin wani babban hari da ya haɗa da makaman linzami na zamani da daruruwan jirage marasa matuka.
Zelenskyy ya ce harin na da muhimmanci ta fuskar diflomasiyya, musamman ganin rawar da Qatar ke takawa wajen sasanta sakin fursunonin yaki.
A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Ukraine Andrii Sybiha ya yi gargadin cewa hare-haren da ke kusa da iyakokin Tarayyar Turai da NATO na barazana ga tsaron yankin Turai baki ɗaya.
Tun da farko, Ma’aikatar Tsaron Rasha ta tabbatar da kai wani babban hari kan cibiyoyin makamashi da wuraren kera jiragen yaki marasa matuka, tana mai cewa martani ne ga wani hari da aka kai kan gidan shugaban Rasha a yankin Novgorod.














