Gabas Ta Tsakiya

Abin da muka sani game da sabuwar tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza da Hamas ta amince da ita

Hamas ta karɓi sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60 da kuma sakin mutanen da ake garkuwa da su.

Newstimehub

Newstimehub

18 Aug, 2025

egypt israel palestinians 12122

Hamas ta shaida wa masu shiga tsakani cewa ta amince da sabon daftarin tsagaita wuta a Gaza, bayan fiye da watanni 22 na yakin da Isra’ila take yi a zirin, kamar yadda wani jami’in ƙungiyar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar 18 ga Agusta.

Masu shiga tsakani na ɓangaren Hamas a birnin Alkahira sun karɓi sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutan ta tsawon kwanaki 60 tare da sakin waɗanda aka kama a rukunai biyu, kamar yadda wani jami’in Falasɗinu ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Tayin yana matsayin tsarin yarjejeniya don fara tattaunawa kan tsagaita wuta na dindindin,” in ji wani jami’in a ranar Litinin, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Tun da fari majiyar ta ce “Hamas za ta gudanar da shawarwari a tsakanin shugabancinta” da kuma tuntubar shugabannin sauran ɓangarorin Falasɗinu don nazarin tayin da masu shiga tsakani suka gabatar”.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila ke shirin fara mamayar ƙasa a birnin Gaza.

Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da ƙungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa mamayar Isra’ila a Gaza za ta haifar da ƙaura da tilasta wa dubban Falasɗinawa barin gidajensu.

Tayin ya samu amincewar gwamnatin Trump, wadda aka gani a matsayin dabarar siyasa daga Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu don tabbatar da kwanciyar hankali a gwamnatinsa ta hanyar faranta wa Ministan Kuɗi Bezalel Smotrich da Ministan Tsaro na Ƙasa Itamar Ben-Gvir rai.

Kwanan nan Smotrich ya yi barazanar yin murabus bayan Netanyahu ya yi ikirarin cewa Isra’ila tana ba da damar agajin jinƙai shiga Gaza – duk da manufofin yunwa da aka ƙirƙira da gangan wanda ya haifar da yunwa mai tsanani a wannan yankin da aka killace.