Duniya Tsaro

New South Wales ta ƙara tsaurara dokokin mallakar bindiga bayan harin Bondi

Jihar New South Wales ta Australia ta amince da sabbin dokoki masu tsauri kan mallakar bindiga da iko kan zanga-zanga bayan harin Bondi da ya kashe mutane 15.

Newstimehub

Newstimehub

24 Dec, 2025

8a541070 3882 4ce1 9fba 9821070d546f.jpg e1766609096572

Gwamnatin jihar New South Wales a Australia ta ɗauki matakin ƙara tsaurara dokokin mallakar bindiga, bayan wani mummunan hari da aka kai wa Yahudawa a wani wurin biki a gabar tekun Bondi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15, lamarin da ya girgiza al’umma tare da tayar da muhawara kan tsaro.

Firimiyan jihar, Chris Minns, ya ce an amince da sabbin dokokin ne domin kare lafiyar jama’a da hana sake aukuwar irin wannan hari, inda sabon tsarin ya bai wa mutum damar mallakar bindiga har guda huɗu, yayin da manoma za su iya mallakar sama da bindiga goma.

Haka kuma, an ƙara wa ’yan sanda iko na hana zanga-zanga, matakin da gwamnatin ta ce yana daga cikin mafi tsauraran dokokin bindiga da aka taɓa aiwatarwa a Australia.

Sai dai wasu masu suka sun bayyana cewa za su ƙalubalanci dokar hana zanga-zanga a gaban shari’a.

Majiyar Labari: BBC Hausa