Manchester City ta hau saman teburin gasar Firimiya ta Ingila na wucin gadi bayan ta doke Nottingham Forest da ci 2-1 a wasan da aka buga a City Ground, inda Rayan Cherki ya zura ƙwallon nasara a minti na 83.
Cherki ne ya fara taimakawa wajen buɗe ci kafin daga bisani ya ci ƙwallon da ta tabbatar wa City nasara, lamarin da ya ba su maki 40, maki ɗaya gaban Arsenal wadda ke da wasa a hannu.
Forest kuwa na ci gaba da zama a matsayi na 17, tana fuskantar barazanar faɗuwa. Nasarar ta zama ta takwas a jere ga City a dukkan gasa, duk da cewa Forest ta yi ƙoƙari ta dawo wasa kafin ƙarshen mintuna.
Majiyar Labari: TRT WORLD














