Sabbin bayanai daga Kebbi sun nuna cewa wani abu ya fashe a Babban Asibitin Ƙaramar Hukumar Bagudo da safiyar Talata, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a, amma rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa babu wanda ya mutu ko ya ji rauni.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, SP Bashir Usman Anisma, ya ce tawagar ƙwararru ta EOD–CBRN ta isa wurin domin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru. Ya bayyana cewa wani gini a sashen gidajen ma’aikatan asibitin ya lalace, amma an kwashe mazauna wurin lafiya lau tun kafin fashewar ta tashi.
Ya ƙara da cewa ba a san musabbabin fashewar ba tukuna, amma bincike ya riga ya fara. Kwamishinan ‘yan sanda ya tura ƙarin jami’an tsaro domin tabbatar da kwanciyar hankali, tare da bukatar jama’a su kwantar da hankalinsu su kuma guji kusantar wurin yayin da ake ci gaba da bincike.














