Nijeriya

Sakon Sabuwar Shekara: Tinubu Ya Ce Za a Tallafa Wa Mutum 1,000 a Kowace Mazaɓa a Nijeriya

Tinubu ya ce gwamnatin Najeriya za ta tallafa wa mutum 1,000 a kowace mazaɓa domin bunkasa tattalin arziki, tare da ƙara ƙaimi wajen yaki da ta’addanci da rage tsadar rayuwa a 2026.

Newstimehub

Newstimehub

1 Jan, 2026

54ced14ac9ec1eafc02607cedd35c51f2d31ea35c8ec1bf51e48909cacf9089a

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnati za ta bunkasa shirin tallafa wa akalla mutum miliyan 10 a fadin ƙasar, ta hanyar taimaka wa mutum 1,000 a kowace mazaɓa cikin mazaɓu 8,809 na Najeriya. Ya bayyana haka ne a cikin sakonsa na sabuwar shekara ta 2025, inda ya ce manufar ita ce ƙara jawo mutane cikin harkokin tattalin arziki da rage talauci.

Tinubu ya ce gwamnati za ta mayar da hankali kan bunkasa noma, kasuwanci, sarrafa abinci da ma’adinai, domin ƙarfafa tattalin arziki. A bangaren tsaro kuma, ya ce dakarun Najeriya na kara matsa wa kungiyoyin ’yan ta’adda, satar mutane da masu tayar da hankali, musamman a arewacin ƙasar, tare da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya.

Shugaban ya ce a shekarar 2026, Najeriya za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro, haɗin kai da tallafa wa jihohi don ƙarfafa rundunar ’yansanda. Ya kuma yi nuni da ci gaban tattalin arziki da aka samu a 2025, ciki har da raguwar hauhawar farashi, ci gaban GDP da bunƙasar kasuwar hannayen jari. Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarin rage tsadar rayuwa a shekarar 2026.

Majiyar Labari: TRT HAUSA