Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana matuƙar damuwa kan harin soji da Amurka ta kai Venezuela tare da kama tsohon shugaban ƙasar Nicolás Maduro da matarsa, tana mai jaddada muhimmancin mutunta ikon ƙasashe da ka’idodin dokokin ƙasa da ƙasa kamar yadda kundin MDD ya tanada. A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce dole ne a kiyaye tsarin doka, martabar ƙasashe, tsaron iyakoki da kuma hakkin al’umma na yin zabi ba tare da tsoma bakin waje ba.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin da ke ɗauke da Maduro ya isa New York bayan harin da aka kai a Caracas, inda aka fitar da shi tare da matarsa aka kuma tuhume su da laifukan miyagun ƙwayoyi da ta’addanci. Wannan mataki ya tayar da cece-kuce a duniya, tare da haifar da tambayoyi kan tsarin siyasar duniya da dokokin kasa da kasa. Bidiyon da aka gani ya nuna Maduro cikin tsatsauran tsaro yayin da ake tafiyar da shi bayan isowarsa sansanin soji a Stewart.
Tarayyar Afirka ta yi kira ga tattaunawa, sulhu cikin lumana da mutunta tsarin mulki a matsayin hanya mafi dacewa wajen magance rikicin Venezuela, tana mai jaddada cewa matsalolin cikin gida na ƙasar za su iya warwarewa ne kawai ta hanyar tattaunawa mai faɗin gaske tsakanin ‘yan ƙasar kanta. Kungiyar ta kuma bukaci dukkan ɓangarori su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani abu da zai ƙara ta’azzara rikici.
A gefe guda, Afirka ta Kudu ta nemi Majalisar Tsaron MDD ta gudanar da taron gaggawa domin tattauna wannan farmaki, tana mai kiran matakin Amurka “take ka’idar kundin MDD” da kuma barazana ga zaman lafiya da daidaito tsakanin ƙasashe. Pretoria ta ce irin wannan amfani da karfi ba tare da izinin doka ba yana iya zurfafa tashin hankali da haifar da rashin tabbas, tana mai tunatar da cewa tarihi ya nuna cewa mamayewar ƙasashe masu cin gashin kansu ba ta kawo mafita mai dorewa.














