Miliyoyin mutane a Sudan na cikin hatsari yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kayan agajin abinci na dab da ƙarewa nan da ƙarshen watan Maris, matuƙar ba a samu sabbin kuɗaɗen tallafi ba.
Daraktan Shirye-shiryen Gaggawa na Shirin Abinci na Duniya, Ross Smith, ya ce hukumar ta riga ta rage yawan abincin da take rabawa, yana mai gargaɗin cewa miliyoyin mutane na iya rasa taimako cikin makonni.
Gargaɗin ya zo ne bayan kusan shekaru uku na yaƙin basasa, wanda ya raba mutane sama da miliyan 11 da matsugunansu tare da jefa fiye da rabin al’ummar ƙasar cikin matsanancin ƙarancin abinci.














