Afirka Siyasa

Burkina Faso: Gwamnati Ta Ce An Dakile Yunkurin Kifar da Mulkin Traoré, Ta Zargi Tsohon Shugaba Damiba

Burkina Faso ta ce ta dakile yunkurin kifar da gwamnatin Traoré tare da zargin tsohon shugaban kasa Damiba da kitsa shirin tare da haɗin gwiwar wasu sojoji da fararen hula.

Newstimehub

Newstimehub

7 Jan, 2026

9307229467fcb2ff6f9996eef71ef6b25d583180e1d931a8da95544e6a42c1ed

Gwamnatin Burkina Faso ta bayyana cewa an dakile wani yunkuri na kifar da gwamnatin shugaba Ibrahim Traoré, tare da zargin tsohon shugaban kasar Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba da kitsa shirin. Ministan tsaro, Mahamadou Sana, ne ya sanar da hakan a daren Talata ta gidan talabijin na kasar RTB, inda ya ce jami’an leƙen asiri sun gano shirin tun kafin aiwatar da shi, tare da nuna godiya ga ƙwarewar hukumomin tsaro.

Ministan ya bayyana cewa an tsara shirin ne ranar Asabar da ta gabata, inda ake zargin za a kashe manyan jami’an gwamnati na soja da fararen hula, tare da kisan Kyaftin Traoré ta hanyar harbi daga kusa ko kuma sanya bam a gidansa. Ya ce shirin ya haɗa da lalata sansanonin jirage marasa matuƙa (drones) da kuma yiwuwar turo dakarun ƙasa daga ƙasashen waje.

A cewarsa, tsohon shugaban ƙasar Damiba ne ake zargi da jagorantar shirin tare da samar da kuɗi, ɗaukar hayar sojoji da fararen hula, da kuma shirya matakan samun goyon bayan jama’a. Sana ya ce saboda dalilai na tsaro, ba za a fitar da cikakkun bayanai kan wasu sunayen ba tukuna, amma gwamnati za ta saki bidiyoyin da ke nuna mutanen da ake zargi da rawar da suka taka a lamarin.

Majiyar Labari: TRT HAUSA