Wani sabon bincike ya nuna cewa fa’idar magungunan rage kiba kan nauyi da lafiyar jiki na gushewa cikin kasa da shekaru biyu bayan an daina shan su. Binciken, wanda aka wallafa a mujallar The BMJ, ya duba bayanan marasa lafiya 9,341 daga bincike 37, inda aka gano cewa yawancin mutane na kara kusan kilo 0.4 a kowane wata bayan sun daina maganin, tare da komawa nauyin da suke da shi kafin jinya cikin kusan shekara 1.7.
Rahoton ya kuma nuna cewa alamomin haɗarin cututtukan zuciya kamar hawan jini da yawan cholesterol, waɗanda suka ragu yayin shan magungunan, su ma na dawowa matakin da suke a baya cikin kimanin shekara 1.4 bayan an daina jinya.
Kimanin rabin marasa lafiyar da aka nazarta sun sha magungunan GLP-1, ciki har da sabbin magunguna masu ƙarfi, inda aka lura cewa duk da saurin rage kiba, nauyin na dawowa da wuri bayan dainawa.
Masu binciken sun bayyana cewa duk da bambancin adadin nauyin da ake rasa, yawancin mutane na komawa matsayin da suke a baya a kusan lokaci ɗaya. Sun kuma lura cewa karin nauyi bayan daina magani ya fi sauri idan aka kwatanta da shirye-shiryen rage kiba ta hanyar canjin halayen rayuwa kawai.
Masu binciken sun ce har yanzu ba a gano dalilin da ya sa wasu mutane ke iya ci gaba da rike nauyin da suka rage ba yayin da wasu ke kasa. Sun jaddada bukatar karin bincike domin fahimtar wane rukuni ne ke cin gajiyar magungunan rage kiba na dogon lokaci.














