Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kusan mutane 7,900 daga cikin ‘yan gudun hijira sun mutu ko suka bace a hanyoyin hijira a duniya a shekarar 2025. Wannan adadi ya ragu idan aka kwatanta da sama da 9,200 da aka samu a 2024, amma duk da haka ana ganin halin na da matukar tayar da hankali. Hukumar kula da ‘yan hijira ta duniya (IOM) ta bayyana cewa wannan na nuna gazawar duniya wajen hana mutuwar da za a iya kaucewa.
Tun daga shekarar 2014, sama da mutane 80,000 ne suka mutu ko suka bace yayin kokarin tsallaka iyakoki a duniya. IOM ta ce raguwar da aka gani a 2025 na iya kasancewa sakamakon karancin mutanen da ke amfani da hanyoyin hijira marasa tsari, musamman a nahiyar Amurka. Duk da haka, an kuma jaddada cewa karancin kudade da ke addabar kungiyoyin agaji na iya hana a tattara cikakkun bayanai, wanda ke nufin adadin na iya zama kasa da ainihi.
A farkon shekarar 2026 ma, an riga an samu akalla mutane 1,723 da suka mutu ko suka bace a irin wadannan hanyoyi. Wadannan hanyoyi, da ke hada Afirka, Gabas ta Tsakiya, Turai da Amurka, na cike da hadurra kamar nutsewar jiragen ruwa, tsananin yanayi, da kuma tashin hankali, musamman a lokacin da kasashe ke kara tsaurara dokokin shige da fice.
Majiyar Labari: AA














