Majalisar ministocin Zimbabwe ta amince da wasu manyan sauye-sauye ga kundin tsarin mulki, matakin da masu adawa suka ce na iya ba Shugaba Emmerson Mnangagwa damar ci gaba da mulki har zuwa 2030. Gyaran, wanda har yanzu ke jiran gabatarwa a majalisa, ya haɗa da tsawaita wa’adin shugaban ƙasa daga shekaru biyar zuwa bakwai, tare da ba majalisa ikon zaɓen shugaban maimakon masu jefa ƙuri’a. Jam’iyyar Zanu-PF mai mulki ta riga ta bayyana “Agenda 2030” a matsayin manufarta tun bara.
Gwamnati ta ce sauye-sauyen za su inganta daidaiton siyasa da ci gaba da manufofi domin kammala shirye-shiryen ci gaba. Daga cikin tanade-tanaden akwai bai wa shugaban ƙasa damar naɗa karin sanatoci 10, wanda zai ƙara kujerun majalisar dattawa. Masu adawa sun dage cewa duk wani gyara da zai shafi tsawaita wa’adin shugaban ƙasa ya kamata a kai shi kuri’ar raba gardama ta ƙasa. A watannin baya, yunƙurin zanga-zanga kan shirin ya gamu da matakan tsaro masu tsauri daga ‘yan sanda.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














