Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya shaida wa shugabannin Afirka cewa rashin wakilci na dindindin da nahiyar ke da shi a Kwamitin Tsaro na MƊD ba abin karewa ba ne. Ya ce lokaci ya yi da za a aiwatar da sauye-sauyen da aka dade ana jinkirtawa, yana mai jaddada cewa Afirka dole ta kasance cikin dukkan manyan shawarwarin duniya da suka shafe ta.
A jawabinsa a wajen taron AU, Guterres ya kuma bukaci daukar matakan gaggawa domin dakatar da rikice-rikice, ciki har da tsagaita wuta nan take a Sudan da sabunta kokarin kawo karshen fada a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Batun tsaro ya mamaye tattaunawar, yayin da shugabanni ke duba manyan matsalolin da suka addabi nahiyar.
A lokaci guda, shugabannin sun mayar da hankali sosai kan tsaron ruwa – taken taron na bana. Jami’an AU sun yi gargadin cewa matsin lambar sauyin yanayi da karancin albarkatu na kara haddasa rashin zaman lafiya. An bayyana ruwa a matsayin ginshikin ci gaba, zaman lafiya, da kwanciyar hankali idan aka sarrafa shi cikin hadin kai.
Firayim Ministan Italiya, Giorgia Meloni, ta ce makomar Turai na da nasaba kai tsaye da zaman lafiya da wadata a Afirka. A yayin taron kuma, an zabi Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye, a matsayin sabon Shugaban AU na 2026, yayin da ake sa ran taron zai tattauna kan Sudan, Sahel, Somalia, sauyin yanayi, da gyaran tattalin arziki.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














