Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa na iya sake kai hare-hare a Najeriya idan har abin da ya kira kisan Kiristoci bai tsaya ba. Trump ya faɗi hakan ne a wata hira da jaridar New York Times da aka wallafa ranar Alhamis.
Ya ce tun da farko ya yi niyyar kai hari guda ɗaya, amma idan aka ci gaba da kashe Kiristoci, Amurka za ta ɗauki ƙarin matakan soja. Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta cewa kashe-kashen da ake yi a ƙasar sun shafi Kiristoci kaɗai, tana mai cewa matsalar tsaro na shafar dukkan ’yan ƙasa ba tare da la’akari da addini ba.
Trump ya kuma ce harin da Amurka ta kai a ranar Kirsimeti an yi shi ne tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya. Duk da amincewa cewa ana kashe Musulmi ma a hare-haren Najeriya, Trump ya dage cewa Kiristoci ne suka fi fuskantar kisa.
A ranar 25 ga Disamba ne Trump ya sanar da kai hari kan abin da ya kira ’yan IS a arewa maso yammacin Najeriya. Daga baya rundunar sojin Amurka a Afirka (AFRICOM) ta ce an kai harin ne a jihar Sokoto, yayin da aka gano ragowar bam a jihar Kwara.
Zargin kisan Kiristoci ya ƙara ƙarfi ne bayan Sanata Ted Cruz ya zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare Kiristoci, zarge-zargen da Abuja ta musanta. Gwamnatin ta ce tana samun ci gaba wajen yaƙi da ’yan ta’adda da kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.














