Gwamnatin Nijeriya a ranar Litinin ta gurfanar da fiye da mutane 400 da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci a gaban alkalan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ana gurfanar da wadanda ake zargin cikin rukuni-rukuni a dakunan kotun daban-daban inda aka dakatar da shari’o’i da dama don ba wa alkalai damar sauraron shari’ar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ne ke jagorantar tawagar masu gabatar da kara, tare da goyon bayan Daraktan Lauyoyin gwamnatin Tarayya, Rotimi Oyedepo, wadanda dukkansu biyu manyan Lauyoyi ne na Nijeriya rike da mukamai na SANs.
Cibiyar ba da taimako kan shari’o’i a Nijeriya ce take wakiltar wadanda ake tuhuma marasa galihu.
Wadanda ake zargin suna fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci, ba da tallafi na kudi ga ta’addanci, da kuma taimakawa da kuma tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayya, John Tsoho, ya nada wasu alkalan kotun don zaman sauraron kararrakin na musamman.
An taɓa irin wannan shari’a ta bai ɗaya a watan Afrilun 2026.
A watan Afrilun 2026 an gudanar da irin wannan zaman shari’a na bai ɗaya a kotun a watan Afrilu, inda Gwamnatin Tarayya ta ce ta yanke wa mutane 386 hukunci kan laifukan ta’addanci.
Daga cikin mutane 508 da ake tuhumarsu a shari’ar, ofishin Antoni Janar ɗin ya yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutane 386, tare da sallamar mutane 8 da kuma wanke mutum 2 daga tuhuma.
Mafi yawa daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, an same su da laifin alaka da ayyukan ta’addanci, kamar taimakawa da sanya kudadensu a ciki, sun kuma fuskanci hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.
Shari’o’in na bai ɗaya sun bayyana yadda gwamnatin Nijeriya ke kokarin hanzarta shari’o’in ta’addanci da aka jinkirta, inda a yanzu ake gudanar da shari’o’i a Abuja maimakon sansanin sojoji da ke Kainji na Jihar Neja.

















