Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta tabbatar da kama ɗaya daga cikin ma’aikatanta bisa zargin sacewa, tsarewa ba bisa ƙa’ida ba da kuma tilasta sauya addini ga wata ƙaramar yarinya a Jihar Jigawa.
Wata Kotun Majistare da ke Hadejia ta bayar da umarnin kama jami’in domin bincike, bayan zargin cewa ya sace Walida Ibrahim, ’yar shekara 16, ya tsare ta tsawon lokaci, tare da tilasta mata sauya addininta daga Musulunci zuwa Kiristanci ba tare da amincewar iyayenta ba.
Ƙorafin ya fito ne daga wani lauya, Gamji Lawchain, wanda ya shigar da kara a madadin mahaifin yarinyar, inda aka ce an sace Walida fiye da shekaru biyu da suka wuce, aka yi lalata da ita, kuma daga baya ta haifi ɗa tana ƙarama.
Masu shigar da ƙorafin sun yi Allah wadai da abin da suka kira mummunan cin zarafi, suna neman a gaggauta dakatar da jami’in daga aiki, a gurfanar da shi a gaban kotu, tare da gudanar da bincike mai zaman kansa kan ofishin DSS da ke Karmajji.
Sun kuma bayyana cewa iyalan Walida sun shiga tsananin damuwa, lamarin da suka ce ya taimaka wajen rasuwar mahaifiyarta.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar 9 ga Janairu, 2026, Mataimakiyar Darakta mai kula da hulɗa da jama’a a hedkwatar DSS ta ƙasa, Favour Dozie, ta tabbatar da cewa ana ci gaba da binciken lamarin, tare da alkawarin bayyana sakamakon binciken ga jama’a.
Ta kuma gyara sunan jami’in da ake zargi, inda ta ce sunansa Ifeanyi Onyewuenyi, ba Ifeanyi Festus ba kamar yadda aka fara ambata a cikin ƙorafin.














