Dubban iyalai ’yan gudun hijira a Zirin Gaza sun wayi gari ba tare da mafaka ba bayan wata mummunar guguwar hunturu ta lalata ko ta kwashe tantunansu, lamarin da ya ƙara tsananta matsalar jin-ƙai da ake fuskanta a yankin.
Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta ce iska mai ƙarfi da ruwan sama mai yawa sun fi shafa tantunan da ke bakin teku, inda iska ta kai gudun kusan kilomita 60 a awa, ta tsaga ko ta kwashe mafakar mutane gaba ɗaya.
Mai magana da yawun hukumar, Mahmoud Basal, ya ce wannan ba matsalar yanayi kaɗai ba ce, illa sakamakon toshe shigar kayan agaji da na gine-gine da Isra’ila ke yi, wanda ya tilasta wa jama’a rayuwa cikin tantuna marasa ƙarfi da gidajen da suka lalace.
Ya ƙara da cewa duk wata sabuwar guguwar iska na rikidewa zuwa bala’in jin-ƙai, kasancewar dubban tantuna da gidaje rabin rusassu na barazanar faɗuwa, musamman yayin ruwan sama da iska mai ƙarfi.
Basal ya bayyana cewa mutane da dama sun tilasta yin zama a bakin teku bayan da hare-haren bama-bamai suka lalata birane da dama, ba tare da wani wuri mai aminci da za su koma ba.
A watannin baya, guguwar iska makamanciya ta haddasa ambaliyar ruwa a tantunan ’yan gudun hijira a Khan Younes, inda aka samu asarar rayuka da dukiya.
Hukumar ta jaddada cewa halin da ake ciki a Gaza ya kauce wa ka’idojin jin-ƙai na duniya, tana mai cewa hakan babban take ne ga dokokin jin-ƙai na ƙasa da ƙasa.














