Wasu ‘yanfashin teku dauke da makamai sun yi garkuwa da matuka jirgin ruwa tara a gaɓar tekun Gabon bayan sun kai hari kan wani jirgin kamun kifi a karshen mako, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar. Lamarin ya faru ne a daren Asabar, inda ‘yanbindiga uku suka kutsa cikin jirgin IB Fish 7 mai tutar Gabon, wanda ke kamun kifi kusan mil bakwai daga Ekwata.
A cewar shugaban rundunar sojin ruwa ta Gabon, Hubert Bekale Meyong, wadanda aka sace sun hada da ‘yan kasar Sin biyar da ‘yan Indonesia hudu. An kuma ce wasu matuka jirgin shida daga Indonesia, China da Burkina Faso sun kasance a cikin jirgin lokacin da aka kai harin, amma ba a sace su ba.
Hukumomi sun gano inda jirgin yake, suka raka shi zuwa tashar jiragen ruwa ta Libreville, sannan aka fara bincike kan lamarin, wanda ke kara nuna barazanar fashin teku a yankin Tekun Guinea.














