A yayin da rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ɗaukar hankalin duniya, kalaman Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, sun bayyana irin yadda Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke ƙara zama saniyar ware a idon ƙasashe da dama, musamman a Turai, sakamakon manufofin soji da ke haddasa mutuwa da barna.
Fidan ya ce manufofin soji na Netanyahu sun sa gyaran dangantaka da Isra’ila ya zama abu mai wuya ga Turkiyya da sauran ƙasashe.
Ya bayyana cewa shugabannin Turai na guje wa mu’amala da Netanyahu a bainar jama’a, har ma da ɗaukar hoto tare da shi, domin hakan ba ya da kyau a siyasa a halin yanzu.
A cewarsa, wannan na nuna yadda Isra’ila ke kara fuskantar killacewa ta fuskar diflomasiyya, inda ko ƙawayenta ke nuna taka-tsantsan.

















