Ankai wani mummunan hari da ya hallaka wata mata da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Charanchi, lamarin da ya girgiza zukatan jama’a tare da tayar da tambayoyi kan tsaro da kare rayukan fararen hula.
Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta ce an kai hari gidan Haruna Bashir da misalin ƙarfe 12:10 na rana a ranar 17 ga Janairun 2025, inda wasu da ba a san ko su waye ba suka kutsa da muggan makamai suka kashe Fatima Abubakar mai shekara 35 da ’ya’yanta shida.
An garzaya da su Asibitin Murtala Mohammed, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsu. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tura tawagar tsaro karkashin jagorancin DCP Lawal Isah Mani, tare da umarnin ACP Wada Jarma na CID ya jagoranci cikakken bincike domin gano da kama masu hannu a harin.














