Nijeriya Tsaro

Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Kisan Uwa da ’Ya’yanta Shida a Kano

’Yan sandan Kano sun kaddamar da bincike kan kisan wata mata da ’ya’yanta shida bayan wani mummunan hari da aka kai gidansu a Dorayi Charanchi.

Newstimehub

Newstimehub

17 Jan, 2026

c97007422365c81f0e217f710fbbab5cee9a3b4f4b9f3ce27ee0bb5bf01c7612

Ankai wani mummunan hari da ya hallaka wata mata da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Charanchi, lamarin da ya girgiza zukatan jama’a tare da tayar da tambayoyi kan tsaro da kare rayukan fararen hula.

Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta ce an kai hari gidan Haruna Bashir da misalin ƙarfe 12:10 na rana a ranar 17 ga Janairun 2025, inda wasu da ba a san ko su waye ba suka kutsa da muggan makamai suka kashe Fatima Abubakar mai shekara 35 da ’ya’yanta shida.

An garzaya da su Asibitin Murtala Mohammed, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsu. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tura tawagar tsaro karkashin jagorancin DCP Lawal Isah Mani, tare da umarnin ACP Wada Jarma na CID ya jagoranci cikakken bincike domin gano da kama masu hannu a harin.

 

Majiyar Labari: TRT HAUSA