Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana baƙin cikinsa matuƙa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran al’ummar ’yan kasuwa a Kano, Alhaji (Dr.) Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a ƙarshen mako.
Shugaban ya ce mutuwarsa babbar asara ce ba ga Kano kaɗai ba, har ma ga Najeriya baki ɗaya, la’akari da irin rawar da marigayi ya taka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗin kan ƙasa.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wata mata, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a unguwar Chiranci, yana mai bayyana lamarin a matsayin dabbanci da rashin imani, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.
Ya kuma yabawa ’yan sanda bisa cafke waɗanda ake zargi tare da bayar da umarnin a gurfanar da su.














