Dakarun Sojin Nijeriya sun sake samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin ta’addanci a Arewa maso Gabas, bayan gano wasu manyan wuraren ɓoye makamai, magunguna da man fetur na Boko Haram a ƙarƙashin ƙasa a yankin Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno, lamarin da ke nuna irin dabarun da ’yan ta’addan ke amfani da su wajen ci gaba da kai hare-hare.
Rundunar Hadin Kai ta Operation Desert Sanity ta kai samame a yankunan Chilaria, Garin Faruk da Abirma bayan samun sahihan bayanan sirri, inda ta lalata sansanonin Boko Haram da ISWAP tare da jawo musu mummunar asara. Jami’in yada labarai Laftanal Kanal Uba Sani ya ce sojojin sama sun bayar da gagarumin tallafi ta hanyar sa ido da bin sahun ’yan ta’adda. A yayin farmakin, an gano harsasai, wayoyi, tutoci, buhun hatsi, magunguna, dizal, da wurin ɓoye man fetur a ƙarƙashin ƙasa da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.














