Bayan rudani da musantawa da aka fara yi kan labarin garkuwa da masu ibada a ƙauyen Kurmin Wali da ke Jihar Kaduna, Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta sake fitowa ta tabbatar da cewa lallai an yi garkuwa da jama’a, lamarin da ya sake jefa al’umma cikin fargaba a yankin da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.
Rundunar ’yan sanda ta ce bayan fara musanta rahoton, bincike mai zurfi ya tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kai hari a ranar Lahadi 18 ga Janairu inda suka sace masu ibada daga wasu coci-coci a Kurmin Wali.
Sufetan ’Yan Sanda Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro da kayan leken asiri domin gano inda aka kai mutanen da kuma kubutar da su lafiya. Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta ce mutane 172 aka sace, inda 9 suka tsere, yayin da aka kai sauran dazukan yankin. Cocin ECWA, Albarka Cherubim da Seraphim 1 da Haske Cherubim da Seraphim 2 na cikin wuraren da harin ya rutsa da su.














