Bayan mummunan kisan gillar da ya girgiza al’ummar Kano, inda wata mata da ’ya’yanta shida suka rasa rayukansu a unguwar Chiranci Dorayi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara ta ta’aziyya ga iyalan, inda ya bayyana matuƙar alhini tare da ɗaukar matakai na jin kai da na shari’a domin tallafa wa marar gata da kuma tabbatar da adalci.
Gwamnan ya amince da shirin walwala ga uban yaran, wanda ya haɗa da daukar nauyin aikin Hajji da Umrah, samar masa da sabon gida, tallafin rayuwa, da taimako domin sake aure.
Ya kuma umurci Babban Lauyan Jihar Kano da Kwamishinan Shari’a da su gaggauta gurfanar da wadanda ake zargi da aikata kisan, yana mai tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin kisa. Gwamnan ya yaba wa ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro kan gaggawa da hadin gwiwar da suka kai ga kama wadanda ake zargi. A matsayin godiya, mahaifin yaran ya ba da filinsa domin gina makarantar Islamiyya ga al’umma.














