Sojojin ƙasa da na sama na Nijeriya sun samu nasarar kashe aƙalla ‘yan ta’adda 61 bayan wani hari da suka kai kan sansanin soji a Malam Fatori, jihar Borno. Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun yi yunƙurin kutsawa cikin sansanin ne da sanyin safiyar Laraba, suna amfani da ƙafa da kuma jirage marasa matuƙa domin karya tsaron wurin.
Sai dai haɗin gwiwar da sojojin ƙasa da na sama suka yi ya dakile harin, inda aka yi musu mummunar ɓarna tare da hana su cimma burinsu. Mahukunta sun ce wannan nasara ta ƙara ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na dawo da tsaro a yankunan da ke fama da hare-hare, musamman a kan iyakokin arewa maso gabas.
A wani ɓangare, rundunar sojin saman Nijeriya ta kuma kai hari a maɓoyar ‘yan ta’adda da ke Abirma kusa da tafkin Chadi, bayan samun sahihan bayanan sirri. An gano cewa ‘yan ta’addan na ɓoye ne a wurare masu cike da ciyayi domin kauce wa ganowa.
Hare-haren sama da aka kai sun lalata kayayyakin ‘yan ta’adda tare da rage karfinsu na kai hare-hare a yankin. Mahukunta sun ce wannan mataki zai taimaka wajen rage barazanar tsaro da ke addabar yankin tafkin Chadi.

















