Gwamnatin Mali ta sanar da ɗaukar matakin raba man fetur da iyaka bayan hare-haren ƙungiyoyin ’yan ta’adda a yankunan kan iyaka sun lalata motocin dakon mai tare da katse hanyoyin shigo da shi ƙasar. Matakin ya biyo bayan dogayen layuka a gidajen mai da ƙarancin fetur da ya shafi rayuwar yau da kullum a faɗin ƙasar.
A cewar hukumomi, sabbin dokokin za su bai wa motoci damar cika tanki sau ɗaya cikin awanni 72, yayin da babura za su iya yin hakan duk bayan awanni 48. Za a kuma yi rajistar lambobin faranti domin sa ido kan yawan man da ake sayarwa, tare da nufin tabbatar da adalci a rarrabawa.
Tun daga watan Satumba, ’yan ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda sun ƙona sama da motocin dakon mai 100, lamarin da ya rage shigo da fetur daga kusan motoci 6,000 a wata zuwa kasa da 2,000 tun farkon wannan shekara. Sojojin Rasha na rundunar Africa Corps suna raka ayarin motocin mai domin kare su daga hare-hare.
Ministan Kasuwanci, Moussa Alassane Diallo, ya ce wannan tsari zai bai wa gwamnati cikakken iko kan gidajen mai, yayin da shugaban ƙungiyar masu shigo da fetur, Ibrahim Touré, ya ce za a iya shawo kan matsalar muddin sojoji na ci gaba da kare motocin mai.
Sai dai direbobin tasi da dama sun nuna damuwa, suna cewa iyakance fetur zai ƙara musu wahala wajen gudanar da aikinsu na yau da kullum.














