Hukumomin Moroko sun yanke shawarar fitar da dukkan mazauna birnin Ksar El Kebir da ke arewacin ƙasar, sakamakon ruwan sama mai yawa da ya haddasa ambaliya. Shugaban karamar hukumar birnin, Mohamed Simo, ya bayyana cewa an dauki matakin ne a matsayin kariya domin kauce wa asarar rayuka, musamman ganin yadda aka samu katsewar wutar lantarki da ruwa.
Rahotanni sun nuna cewa birnin na da kimanin mazauna 120,000, kuma an fara fitar da su ne tun bayan samun gargadi na karin ruwan sama mai tsanani a yankin.
A cewar ‘yar majalisar dokoki Zineb Simo, an dauki matakin ne bayan hasashen cewa ruwan dam din Oued El Makhazine zai kara karuwa, lamarin da zai iya tsananta ambaliyar kogin Loukkos. Tun da farko, hukumomi sun riga sun fitar da mafi yawan mutanen da ambaliya ta shafa, inda aka kiyasta cewa sama da kashi 70 cikin 100 na jama’ar birnin sun bar muhallansu kafin a yanke shawarar fitar da kowa gaba daya.
Gwamnati ta kuma dakatar da karatu a makarantun yankunan da abin ya shafa, yayin da sojoji ke ci gaba da shirin kai dauki ga wadanda ambaliyar ta rutsa da su a sassan kasar Moroko.
Majiyar Labari: AA














