Rundunar sojin Mali ta bayyana cewa ta kashe mutane da dama da ake zargi ‘yan bindiga ne a jerin hare-haren da aka kai a yammacin birnin Ségou. A cewar Babban Hafsan Sojoji, hare-haren sun biyo bayan sa-ido na yankin da aka gudanar a ranar 7 ga Fabrairu, inda aka gano wasu kungiyoyi dauke da makamai suna boyewa a dazuka da ke yankin.
Sanarwar ta ce a hari na farko, an kai farmaki kan wata kungiyar kimanin mutum 15 da aka gano suna kokarin fakewa, kuma an “kawar da su gaba daya”. Daga bisani, wani hari ya hallaka wasu goma sha biyu yayin da suke kokarin sauka da kwale-kwale a gabar hagu ta Niger River, tare da lalata kayayyakin tallafin su.
A wannan yankin ma, sojojin sun ce sun gano wata kungiyar kusan mutum 10 da ke motsi a kan babura, inda aka kai musu hari aka kuma kawar da su. Rundunar ta jaddada cewa wadannan ayyuka na daga cikin shirin tsare yankuna da dakile motsin kungiyoyin dauke da makamai.
Hafsan sojojin Mali ya ce za a ci gaba da irin wadannan hare-hare a fadin kasa, yana mai cewa “ayyukan bincike da kawar da ‘yan ta’adda na gudana a ko’ina.” Mali dai ta shafe fiye da shekaru goma tana fuskantar matsalar rashin tsaro, musamman a yankunan tsakiya da arewa, inda hare-haren kungiyoyin makamai ke barazana ga fararen hula da jami’an tsaro.
Majiyar Laabari: AA














