Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta amince da abin da ya kira “bukatu barkatai” ba a tattaunawar nukiliya da Amurka. Ya jaddada cewa Iran a shirye take a tantance shirinta na nukiliya, yana mai cewa ba ta da niyyar kera makamin nukiliya.
Wannan na zuwa ne bayan dawowar tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu a makon jiya, karo na farko tun bayan rikicin da ya biyo bayan yaƙin Iran da Isra’ila a bara. Da yake magana a Azadi Square a Tehran, Pezeshkian ya ce Iran za ta ci gaba da tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya a yankin, amma ba za ta mika wuya ga matsin lamba ba.
Iran na son a mayar da hankali kan shirin nukiliya, yayin da Amurka ke neman a tattauna batun makamai masu linzami da tasirin Iran a yankin. Kalaman shugaban sun zo ne a yayin bikin cika shekaru 47 da juyin juya halin 1979, inda aka lura da tsauraran matakan tsaro bayan zanga-zangar da aka yi a watannin baya.
Majiyar Labari: TRT WORLD














