Tarayyar Turai (EU) ta sanar da fitar da sama da euro miliyan 81 domin tallafawa al’ummomin da rikicin Gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) ya shafa, inda matsalar tsaro da ta jin kai ke ci gaba da tsananta. Sanarwar ta zo ne a Kinshasa yayin ziyarar Hadja Lahbib, kwamishinar EU mai kula da daidaito da shirye-shiryen tunkarar rikice-rikice.
Kudin da ya kai euro miliyan 81.2 zai mayar da hankali kan bukatun gaggawa na ‘yan gudun hijira da sauran jama’a masu rauni, musamman a fannoni kamar abinci, ruwan sha, matsuguni da kiwon lafiya. EU ta bayyana cewa euro miliyan 68 za su tafi kai tsaye ga ayyukan agaji a cikin DRC.
Tallafin zai hada da samar da abinci na gaggawa, kula da lafiya da abinci mai gina jiki, dawo da hanyoyin ruwa da tsafta, da kuma karfafa kariyar fararen hula, musamman mata da yara da ke fuskantar barazanar tashin hankali.
Sauran euro miliyan 13.2 za su taimaka wa ‘yan gudun hijirar Kongo da ke kasashe makwabta kamar Burundi, Rwanda da Tanzania, tare da inganta hadin gwiwar yankin wajen tunkarar rikice-rikice. EU ta tuna cewa sama da mutane miliyan 21 a DRC na bukatar agajin jin kai, daya daga cikin manyan rikice-rikice a duniya.
Majiyar Labari: AA














