Gwamnatin India ta sanar da gyaran yarjejeniyar haraji da France, inda ta cire sharadin most-favoured-nation daga cikin dokokin da ke jagorantar hulɗar harajin kasashen biyu. Ma’aikatar kudi ta ce an dauki matakin ne a matsayin wani bangare na sabunta tsarin haraji.
Haka kuma, gwamnati ta sake fasalin yadda ake harajin kudin rabo (dividends). Sabon tsarin ya maye gurbin tsohon kason haraji na kashi 10% daya tak, da wani tsari mai rarrabuwa. A karkashin dokar, masu hannun jari da ke rike da akalla kashi 10% na jarin kamfani za su biya haraji 5%, yayin da sauran masu zuba jari za su biya 15%.
Rahotanni sun nuna cewa wannan gyara na da alaka da yarjejeniyar da kasashen suka cimma don rage harajin rabon da rassan kamfanonin Indiya ke biya ga iyayen kamfanoni a Faransa. Wannan ya biyo bayan tattaunawar da aka dade ana yi kan sabunta yarjejeniyar tun daga shekarar 1992.














