Wani rahoto na shekara-shekara ya nuna cewa fiye da mutum 65,000 daga Yahudawa sun shiga harabar Masallacin Ƙudus a shekarar 2025, adadin da ya karu da kashi 22% idan aka kwatanta da 2024. Aƙalluman, kamar yadda Gidauniyar Birnin Ƙudus ta Ƙasa da Ƙasa ta wallafa, sun dogara ne kan bayanan da aka samo daga kwamitin Waqf na Musulunci da ke kula da wurin.
Rahoton ya ce ziyara mai alaƙa da ‘yan siyasar Isra’ila ta ƙaru sosai, inda aka samu kutse na siyasa har sau 20 a 2025, daga sau tara a shekarar da ta gabata. An ambaci wasu manyan jami’ai, ciki har da Itamar Ben-Gvir, cikin waɗanda suka shiga harabar.
Takardar ta kuma yi nuni da sabbin matakan da hukumomin Isra’ila suka ɗauka kan tsarin shiga, ciki har da tsawaita awannin ziyara da ƙara adadin masu shiga a rukuni guda. Masu fitar da rahoton sun bayyana hakan a matsayin sauyi ga daɗaɗɗiyar matsayar wurin mai tsarki.
Baya ga batun harabar, rahoton ya tattauna matsin lamba da Falasɗinawa ke fuskanta a Gabashin Birnin Ƙudus, ciki har da batutuwan takardun zama, ilimi da talauci. A gefe guda kuma, bayanan Isra’ila sun bayar da adadi mafi girma, suna cewa sama da mutum 76,000 sun ziyarci wurin a 2025.














