Ana fuskantar rashin tabbas a tsakanin ‘yan Nijeriya da ke shirin tafiya Umara zuwa Saudiyya bayan rikicin da ya barke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya fara shafar zirga-zirgar jiragen sama. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar masu tafiya Umara a karshen watan Ramadan, lokacin da yawanci mahajjata ke yawaita zuwa Saudiyya domin gudanar da ibada.
Rikicin da ke ci gaba a Gabas ta Tsakiya ya jawo rufe wasu sararin samaniya a kasashe kamar Iran, Isra’ila, Iraq, Syria, Kuwait, Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Wannan mataki ya haifar da katsewar wasu tafiye-tafiyen jiragen sama, inda kamfanonin jiragen sama da dama ciki har da Emirates, Qatar Airways, British Airways da Turkish Airlines suka soke wasu daga cikin tafiyarsu.
Sai dai har yanzu Saudiyya ba ta sanar da rufe sararin samaniyarta ba, kuma jiragen sama na ci gaba da sauka a kasar. Duk da haka, halin da ake ciki ya sa wasu maniyyata suna sake tunanin tafiyarsu, yayin da wasu da suka riga suka shirya tafiya ke fargabar makalewa a hanya idan rikicin ya kara tsananta.
Wani maniyyaci daga Kano, Alhaji Auwal Sani, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an soke jirgin da zai bi na Qatar Airways, kuma har yanzu bai samu biza ba duk da shirinsa na tafiya tare da iyalinsa.
Haka kuma wani mai shirin tafiya Umara, Salihu Shu’aibu, ya ce halin da ake ciki ya jefa shi cikin tashin hankali saboda rashin tabbas kan yadda tafiyarsa za ta kasance.














