An ji kararrawar gargadin gaggawa a kasar Bahrain a daren Talata yayin da hukumomi suka gargadi mazauna kasar da su nemi mafaka sakamakon hare-haren da Iran ke kaiwa a yankin. Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta sanar da hakan ta wani sako da ta wallafa a shafin X, inda ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da garzayawa zuwa mafakar da ta fi kusa da su.
Sanarwar ta ce an kunna kararrawar gargadi domin fadakar da jama’a game da barazanar hare-haren da ake zargin suna da alaka da matakan ramuwar gayya da Iran ke dauka. Duk da haka, hukumomin Bahrain ba su fitar da karin bayani kan girman barazanar ko irin wuraren da abin ya shafa ba.
Tashin hankalin a yankin Gabas ta Tsakiya ya kara kamari ne bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a karshen mako, inda rahotanni suka ce mutane kusan 800 ne suka mutu ciki har da jagoran addini na Iran, Ali Khamenei, da wasu manyan hafsoshin soja.
Bayan wannan hari, Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami, inda aka ce sun nufi Isra’ila da wasu kasashen yankin Tekun Fasha da ke dauke da sansanonin sojojin Amurka.














