Akalla sojoji 15 ne suka mutu bayan ‘yan ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda suka kai hari kan wani sansanin soji a arewacin Jamhuriyar Benin. Harin ya faru ne a ranar Laraba a wani sansani da ke kusa da Kofouno, yankin da ke kan iyakar Benin da Jamhuriyar Nijar.
Rundunar sojin ƙasar ta ce harin ya kuma jikkata wasu sojoji biyar, amma ba sa cikin haɗarin mutuwa. Wata majiya ta soji ta bayyana cewa harin ya yi muni sosai, kuma sojoji na ci gaba da aikin tsaro domin tabbatar da cewa yankin ya koma cikin kwanciyar hankali.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da share yankin da kuma bincike, yayin da hare-haren ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ke ƙaruwa a yankunan iyakar Sahel a ‘yan shekarun nan.














