Nijeriya

Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yanbindiga 45 a Katsina, daga ciki har da Kachallah Alti

Kachallah Alti, wanda gawurtaccen ɗanbindiga ne, ɗan’uwa ne kuma mataimaki ga ƙasurgumin shugaban ’yanbindigan nan Adamu Alieru inda Altin ya fara addabar ƙauyuka bayan mutuwar ɗan’uwansa Kachalla Dan Isihu

Newstimehub

Newstimehub

7 Mar, 2026

4e5b73e8a7d7bf1e98f1d08fe537e4e2db8fba1cc6f04e7a3684161c23a57999

Dakarun Sojojin Nijeriya sun kashe wasu da ake zargin ’yanbindiga ne guda 45 a yayin wata musayar wuta da ta faru a Ƙaramar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.

Majiyoyin tsaro sun ce wannan farmaki ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu kan ’yanbindiga da ake zargin suna aiki a wasu sassan Katsina da maƙwabciyarta Jihar Zamfara.

Daga cikin waɗanda aka kashe a wannan farmaki akwai wasu manyan shugabannin ’yanbindiga biyu waɗanda suka haɗa da Alti, wanda ɗan’uwa ne kuma mataimaki ga ƙasurgumin shugaban ’yanbindigan nan Adamu Alieru, sai kuma wani kwamanda da ake kira Damale.

Majiyoyin sun ce wannan fafatawa ta faru ne bayan wasu ’yanbindiga a kan babura kuma ɗauke da manyan makamai sun kai hari ƙauyen Alhazawa a Ƙaramar Hukumar Musawa a ranar 5 ga Maris, inda suka kwashe shanu na mazauna yankin.

Rahotanni sun ce al’ummar yankin tare da wasu ’yanbindiga da suka tuba sun yi turjiya ga harin, inda suka kashe ’yanbindiga huɗu tare da ƙwato shanun da aka sace, aka mayar wa masu su.

Sai dai an ce ’yanbindigar sun sake haɗuwa tare da komawa da yawa a ranar 6 ga Maris, inda ake zargin sun shirya kai wani harin ramuwar gayya.

Yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Musawa ta cikin Maidabino A Ward, sun ci karo da dakarun sojoji da aka jibge a sansanin Forward Operating Base (FOB) da ke Dan Ali a Ƙaramar Hukumar Danmusa.

Hakan ya janyo wata mummunar musayar wuta inda dakarun sojojin suka yi nasarar rinjayar ’yanbindigar tare da kashe 45 daga cikinsu.

Sai dai a ɓangaren sojoji ma an samu asara, inda sojoji uku suka rasa rayukansu a yayin wannan fafatawa.

Bincike ya nuna cewa Alti ya fara gawurta matuƙa a ayyukan ƙungiyar ’yanbindiga bayan mutuwar ɗan’uwansa Kachalla Dan Isihu, wanda jami’an tsaro suka kashe a baya a wasu hare-haren kan ’yanbindiga.

An ce Alti ne ke tsara hare-hare da dama a kan al’ummomi, musamman a yankin Danjibga na Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Majiyoyin tsaro sun ce dakarun sojoji sun ƙara tsaurara ayyukan bincike a yankin domin bin diddigin sauran ’yanbindigar da suka tsere tare da rusa cibiyoyin ayyukansu.