Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas ƙarƙashin ayyukan Operation Desert Sanity da Siege Operations sun kashe ’yan ta’adda 12 tare da ƙwato bindigogin AK-47 da harsasai a safiyar ranar Jumma’a.
An gudanar da aikin ne a yankin Kirawa da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, lokacin da waɗanda ake zargin ’yanta’adda ne suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin dakarun Bataliya ta 153.
“Bayan artabun, dakarun sun tabbatar da kashe ’yanta’adda 12, yayin da aka ga wasu da dama suna guduwa da raunukan harbi kamar yadda jinin da suka bari a hanyoyin da suka gudu ya nuna,” in ji Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, a wata sanarwa.
Ya bayyana cewa an ƙwato kayayyakin yaƙi da dama.
“Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin AK-47, na’urorin harba rokoki, harsasai, da bindigar PKT, lamarin da ya ƙara raunana ƙarfin yaƙin ’yanta’addan a yankin,” in ji sanarwar Uba.
Da yake bayanin yadda aikin ya gudana, ya ce dakarun sun yi nasarar daƙile harin da ake zargin mayakan Daesh-WAP/Boko Haram ne suka kai a yankin Kirawa da ke yankin aiki na Sector 1 na OPHK a safiyar ranar 22 ga Mayu, 2026.
“Wasu daga cikin waɗanda ake zargin ’yanta’addan ne sun yi ƙoƙarin kutsawa wuraren da dakarun Bataliya ta 153 da sauran jami’an tsaro ke tsare a kan iyakar Nijeriya da Kamaru,” in ji shi.
“An gano harin cikin gaggawa tare da mayar da martani da ƙarfin wuta daga dakaru da jami’an CJTF masu tsaro, waɗanda suka tsaya tsayin daka suka daƙile harin.”
A cewarsa, hakan ya tilasta wa ’yanta’addan janye harin cikin ruɗani zuwa yankin Kamaru bayan sun yi asarar mayaƙa da dama a yayin fafatawar.
















