Nijeriya

‘Yanbindiga a Nijeriya sun kashe manoma 17 a Jihar Zamfara

Yanbindiga kan babura da dama sun kai hari ƙauyen Tungar Baure a Jihar Zamfara inda suka buɗe wuta a ranar Jumma’a, in ji Yahaya Abubakar Yari, mai kula da harkokin siyasa na Karamar Hukumar Talata Mafara.

Newstimehub

Newstimehub

27 Jun, 2026

4eb6ca003452f9e87a232a54f4e146a989b2618ab0549ed96fa4e79faa0b9fca

‘Yanbindiga sun kashe manoma 17 a wani harin da suka kai wa wata al’ummar da ke cikin karkara a arewa maso yammacin Nijeriya, in ji wani jami’i a ranar Asabar.

Tashin hankali a yankin ya tilasta wa yawancin manoma barin gonakinsu, yayin da Asusun Bayar Lamuni na Duniya (IMF) ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan hare-hare na iya “ƙara talauci da rashin wadatar abinci” a ƙasar.

Yanbindiga kan babura da dama sun kai hari ƙauyen Tungar Baure a Jihar Zamfara inda suka buɗe wuta a ranar Jumma’a, in ji Yahaya Abubakar Yari, mai kula da harkokin siyasa na Karamar Hukumar Talata Mafara, a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

“‘Yan ta’adda sun kashe mutane 17 kuma sun sace wasu da ba a fayyace adadinsu ba a harin da aka kai ƙauyen,” in ji Yari, wanda ya halarci jana’izar waɗanda abin ya rutsa da su.

Harin ya faru ne a ƙaramar hukumar da mataimakin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle ya fito, wanda ya taɓa yin alƙawarin tura sojoji 2,000 don taimakawa wajen yaƘi da ƙungiyoyin masu laifi.

Wani bidiyo da wakilin AFP ya gani ya nuna ɗaruruwan mazauna Tungar Baure da suka fusata inda suka toshe babbar hanya a zanga-zangar da suka yi kan kisan, suna neman a tura sojoji don su kare su.

A ranar 12 ga Yuni, ‘yanbindiga sun kashe wasu manoma 17 kuma sun jikkata wasu biyar yayin da suke aikin gona a wani ƙauye da ke makwabtaka da Ƙaramar Hukumar Maradun, a cewar jami’an yankin da mazauna.