Iran ta fara tunanin saka kuɗin hanya wanda jiragen ruwan da suke son wucewa ta Mashigin Hormuz za su biya, kamar yadda kafofin watsa labarai na Iran suka ruwaito a ranar Alhamis.
A cewar kamfanin dillancin labarai na ISNA, an gabatar da wani daftarin doka domin fara amsar kuɗaɗe ga jiragen ruwan da ke son bin hanyar ta cikin teku, wadda ita ce hanya mafi muhimmanci a duniya wurin jigilar makamashi.
Wani ɗan majalisa daga Tehran ya ce wannan shawarar na nufin tilasta biyan kuɗade da haraji ga Iran idan an yi amfani da mashigin a matsayin “hanyar wucewa mai aminci” don jigilar kaya na teku, safarar makamashi da kuma abinci.
Ya ce ƙasashen da ke amfana daga tsaron da suke samu idan za su wuce ta mashigin “ya kamata su biya kuɗi da haraji ga Iran.”
Wannan shawarar ta bayyana ne a daidai lokacin da tashin-tashina a yankin ya ƙaru tun bayan Isra’ila da Amurka sun ƙaddamar da farmakin haɗin gwiwa kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya kashe kusan mutane 1,300 zuwa yanzu, ciki har da Jagoran Addini Ali Khamenei.
Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami a faɗin yankin, kuma ta kusan rufe mashigin Hormuz gaba ɗaya — wata muhimmiyar hanyar jigilar mai da ke gangar mai aƙalla miliyan 20 ke wucewa a duk rana, kusan kaso 20 kenan na ɗaukar kimanin baril miliyan 20 a rana da kusan kashi 20 cikin 100 na cinikayyar iskar gas na LNG da ake amfani da shi a duniya.














